Intro Dadi na Shine Yesu Dadi na Verse 1 Uba alherin ka gareni a yau sun fi gaban misali Yesu ni na mika ma godiya ta ayau domin kaunar ka To me ya maida ni dacecce ayau gaban kursiyin ka Ni zan mika ma dumbin godiya ta domin dumbin kaunarsa Chorus Oh Ya yesu Lura da ni a cikin tafiya ta da kai Lura da ni ka da inyi tuntube Verse 2 Uba kaunar ka ne ya sa mun taru a yau a gaban ka Bari zumuncinda ka sa tsakanin mu shi tabbata har abada
Kada wata kunci ko tsananin rayuwa ta raba mu da kai Don iyakan begen mu na can sama a wurin ka maiceto Bridge Dadi na Shine Yesu Dadi na Verse 3 An tozarta mani a cikin rayuwa ta ya Yesu in ban da kai Rayuwa ta zama abin tausayi Uba a duniyannan Ina mafaka ya Yesu in banda kai wurin wa zani Don iyakan begen na na can sama a wurin ka maiceto